Ya ga tsohon jarumi Ahlan ta yi saukar karatun Al-kur'ani

Picture source : Ali Nuhu instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin manyan jarumai da Kannywood ta yi yayin su a shekarun baya kuma malami a makarantar Sa'adatu Rimi wato jarumi Ahlan, ya taya Yar sa bikin sauke karatun Alkur'ani mai girma da ta yi cikin makon nan.

Jarumin ya baiyana hakan ne cikin wani rubutu da ya yi a kasan hoton sa da yar sa tare cikin haya iri daya wato (Anko), tare budeddiyar wasiga ga masoyan sa da Yar ta sa cikin harshen turanci Kamar haka:

Fassara kalaman Ahlan:
Bubu wani abu a rayuwar mahaifi, mai tarin farin ciki, mahimmanci da kuma daraja da ya kai ganin nasara da cigaban yayan sa wajan zamowa abun da ya ke fatan su zama.

Ina alfahari da ke "Ya ta" yar baiwa ta musanman (a gafarci kalamai na idan sun yi kama da san kai), wacce ta yi saukar Alkur'ani mai girma. Matsayi mara kwatantuwa da ko wani mahaifi zai so wa yayan sa. Gashi a fannin karatun boko ma, kwanan nan ta kammala jarrabawar fita daga Sakandari ta (WAEC) da sakamako mafi daraja ta distinction har guda tagwas cikin tara (8 Distinction), yanzu kuma ga wannan babban rabon na sauke Alkur'ani mai girma.

Hakika Allah ka na so na da alheri kuma ina godiya ga daukacin wadan da duk su ka halacci wajan saukan da kuma wadan da su ka turo da sakon taya murna da addua. Allah ya saka wa kowa da alheri.


Jarumi Ali Nuhu na daga cikin jaruman da su ka daura hoton jarumi Ahlan da yar sa dan taya su murna.

Leave your comment