Mawaki Nura M. Inuwa ya hadu da wata babbar masoyiyar sa

Picture source : official Inuwa's instagram handle

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin salon Nanaye daga manana'antar Kannywood Nura M. Inuwa ya yi ido hudu da wata baiwar Allah da ke matukar kaunar sa a cikin makon nan da mu ka yi bankwana da ita a cikin watan Maris 2021. Mawaki Nura ne ya sanar da wannan haduwar a shafin sa na instagram a lokacin da ya wallafa hoton su tare da wannan baiwar Allah mai suna Hasfa wacce aka fi sani da Nuriyya.


Wani abun daukan hankali shi ne inda mawakin ya baiyana a cikin bayanan sa cewa, ko da su ka hadu da wannan masoyiyar ta sa, sai ta yi sujjada ga Allah dan nuna godiyar ta gare shi bisa hada ta da ya yi da gwanin ta, daga bisani kuma ta fashe da kukan murna dan shaukin ganin mawaki Nura M. Inuwa kusa da ita.

Mawakin ya yi wa wannan masoyiyar sa godiya matuka tare da adduar Allah ya bata miji na gari tare da biyan duk bukatun ta.

Nura wanda har yanzu masoya ke cigaba da dakon fitowar ssbuwar wakar sa mai taken "Ni da ku", daya ne daga cikin manyan mawaka da manana'antar Kannywood ke alfahari da su wajan daga darajar ta da irin wakokin su da ke cigaba da karade ko ina.

Leave your comment