Jaruma Mansura Isah ta yi rabon magunguna ga mabuka

Photo source : Mansura's official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram


Fitacciyar tsohuwar jarumar kannywood Mansura Isah kuma mata ga shahararren mawaki, jarumi a Nollywood da Kannywood wato Sani Danja tayi rabon magunguna ga mabukata a cikin karshen makon nan da muke ciki.

Rabon magungunan ya zo ne kwanaki kadan bayan baiyanar wani annoba da ta faru a jihar Kano, inda aka samu mutuwar mutane da dama da kuma tarin wasu a kwance kan gadon asibiti, sakamakon wani gurbataccen sinadarin da ake sanyawa abun sha da ake zargin ya yi expire ne.

Jarumar ta yi wannan magungunan ne tare da rabon kayan abinci ga mabukata, a matsayin na ta gudunmawar ga Al'ummar da jarumar ta fito daga cikin su kafin samuwar daukakar ta.

Acikin fefen bidiyan da jarumar ta wallafa a shafin ta na instagram, an nuno jarumar ta na mika magungunan ga mabukata tare da shawartar su da su nemi likita kafin su yi anfani da magungunan. Kasancewa ita ba likita ba ce kuma ba ta zo wajan rabon da likitoci ba.

Da dama daga cikin masoyan ta ne su ke kara yabon jarumar tare da shawartar ta nan gaba idan zata bayar da irin wannan tallafin, to ta je da likitoci dan samun sauki wajan ssmun bayanan yadda ya dace a yi anfani da magungunan.

Leave your comment