Mawaki Mic Flamer ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Picture source: Mic Flamer's official Facebook account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Babban mawaki fitacce kuma daya daga mawakan da su ka yi tashe a shekarun baya a masana'antar Hausa Hip Hop Mic Flamer ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a karshen satin nan da mu ke ciki.

Mawakin ya wallafa hoton sa ne a shafin sa na Facebook inda a kasan hoton mawakin ke godiya ga daukacin masoyan sa, abokai da yan uwa da su ka daura hotunan sa a kafafan sadarwa mabanbanta tare da ma sa adduar dacewa da kuma karin shekaru ma su albarka.


Mic Flamer wanda a halin yanzu ya dan ja baya da masana'antar Hausa Hip Hop din, ta hanyar daina sakin wakokin kan sa ko kuma na hadakan mawaka, ya yi suna ne shekaru da su ka wuce da fitaccen wakar sa mai taken "Takalmi na", wanda kusan daga kan wakar ne mawakin ya fara baya baya da harkar.


Mic Flamer ya fito a cikin wakar K Arrows ta hadakar mawaka 12 mai taken" Babban Magana", wanda kusan daga ma kanta ne mawakin bai sake wata waka ba, duk da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin shi da nawaka da dama musanman mawakan ungwar Sabon Gari bayan mawakin Zoo road ne kamar yadda ungwa ta banbanta wadan nan mawakan.

Mu na wa mawaki Mic Flamer fatan dacewa da kuma rayuwa mai cike da farin ciki mara yankewa.

Leave your comment