Mawaki Dan Sa'a ya yi jaje ga yan kasuwa a jahar Katsina

Picture source: Dan Sa'a official Facebook account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram


Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan jahar Katsina kuma ma'aikacin radiyo wato Dan Sa'a ya mika sakon jaje ga yan kasuwan da gobarar da aka yi jiya ya shafe su, wannan gobara ya faru jiya litinin 22 ga watan Maris 2021 da safiyar jiya ne a babban kasuwar jahar Katsina ta central market. Ya yi wannan jaje ne a shafin sa na Facebook yau talata.

Tin da gobarar ta fara ne aka yi kokarin kawo dauki cikin gaggawa, inda aka kira yan kwana kwana dan kawo dauki, amma hakan ya citira, wanda hakan ya jawo neman karin agaji daga wasu mutunan na gari da su kan su yan kasuwan.

Yan kwana kwanan da su ka kawo dauki dan kashe wannan gobarar har da wasu daga kananan hukumomi irin su karamar hukumar kankiya da sauran kananan hukumomi.

Kamar yadda mawaki Dan Sa'a ya sheda wa majiyar mu ta Madubi Naija ta wayar talho, ya baiyana wa majiyar mu cewa ya na kan hanyar zuwa makaranta ne ya hango wannan gobara daga cikin kasuwar ta central market, kuma ko bayan dawowar sa daga makaranta da sauran gobarar.

Kimanin shaguna 200 ne su ka kone har da wanyan shagunan ajiyan kaya da kuma wani shagon sayar da gwalagwale. Wani shashin bankin da ke cikin kasuwar ta kama da wuta amma ba ta yi tasiri ba Allah ya takaita.

Leave your comment