Bayan da su ka shirya tsakanin su kuma su ka yi waka tare, sun dawo sun yi bidiyan wakar.

Picture source: official Instagram account of Madox

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Matasan mawakan nan biyu da su ka yi rigima tsakanin su har da kokowa a kwanakin baya a cikin wani hotel, wato Madox Tbb da Mr 442, wanda kuma su ka shirya tsakanin su daga baya har su ka yi waka tare mai taken "Sai Monday", sun dawo sun yi bidiyan wakar.

Bidiyan wanda ya fita a yau ranar Litinin 22 ga watan Maris 2021 a shafukan sauke wakoki daban daban, ya fara jan hankalin mabiya wakokin Hausa Hip Hop daga sassan Najeriya. Musanman yadda wannan bidiyan ya fito a lokaci dan kalilan bayan fitan audio din.

"Sai Monday" waka ce da ke da irin salon mawakan kudu irin su Naira Marley, Zlatan, Mr Real da dai sauran su, kuma wakar ta karkata ne ga nishadantar da matasa ne musanman idan aka yi la'akari da kalaman da mawakan biyu su ka yi anfani da su a cikin wakar.


Madox dan jihar Kano ne mazaunin garin Zaria Inda mawakin ke karatu a halin yanzu a jamiyar Ahmadu Bello wato A.B.U Zaria. Shi kuma Mr 442 mawaki ne dan garin Zaria da ke jihar Kaduna, wadan nan mawaka biyu na daga cikin matasan mawaka da ake sa rai za su yi tashe a cikin shekarar nan ta 2021.

Leave your comment