Jiya anyi bikin ranar Uwa ta duniya, jarumai da mawaka sun shiga cikin wannan bikin.

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram


Jiya lahadi 14 ga watan Maris ta shekarar 2021 ne, a ka yi bikin ranar Uwa (mahaifiya) ta duniya, wanda kuma miliyoyin mutane ne su ka shiga sahun ma su wannan biki, kuma a cikin su har da mawaka da jarumai da dama da suma su ka yabi ta su mahaifiyar.

A bangaran jarumai yan fim, babban jarumi kuma ma'aikacin gidan talabishan ta Arewa24 wato TY Shaban, ya daura hoton mahaifiyar sa wace Allah ya yi wa rayuwa da jumawa, inda ya ke mata adduar samun rahma da gafarar ubangiji.

Kamar yadda a bangaran mawakan Hausa na salon Nanaye, fitaccen mawaki Ahmed Delta shi kuma ya daura hoton wani rubutaccen sakon yabo ga mahaifiyar sa a shafin sa na Instagram, kuma ya baiyana cewa wannan baitin waka ce da ya rubuta wa mahaifiyar sa kuma zai raira ta kwanan nan.

Su ma a bangaran mawakan Hausa Hip Hop, mawaki Feezy dan jihar Kaduna ya daura hoton bidiyan wani waka dauke mai suna "Mamma" da su ka yi tare da Zayn Africa da shi Feezy din da kuma Gee boy. Duk a cikin bikin ranar Uwa ta duniya.

Kamar yadda shi kuma shahararren mawaki marubuci kuma jigo a cikin matasan mawakan Hausa Hip Hop, wato Dabo Daprof (Mister Ladagoma) shi kuma ya wallafa sakon alhini da kewa ga marigayiyar mahaifiyar sa da ta rasu sama da shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai da ya wuce. Inda mawakin ke baiyana halin da ya ke ciki na rashin Uwa duk kuwa da shekarun sa a duniya da kuma daukakar sa.

Hakika mahaifiya ta kasance babbar kyauta kuma rufin asiri ga duk mai ita, kuma wannan ne ya sa ya ke da kyau mutane su dage wajan martaba mahaifiyar su idan ta na raye.

Idan kuma ba ta raye, sai a dage wajan yi mata addua tare da rokan mata rahma da gafarar Allah. Domin babu wani gata da mutun ke da shi kamar iyaye. Kuma matsayi da rawar da mahaifiya ke takawa ba karama ba ce a rayuwar mutun.

Leave your comment