Ni kyakkyawa ne -Uniquepikin

Photo source: from  Uniquepikin's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitaccen Matashin mawakin zamani na gambara wato Hausa Hip Hop kuma makadi Mubarak Uniquepikin ya kuran ta kan sa ta hanyar rabon halittar da Allah ya mai, inda ya ce shi kyakkyawa ne. Mawakin a shafin sa na Facebook inda ya baiyana a kalaman sa cewa "Ni kyakkyawa ne kuma babu wani abu da duniya za ta ce a kai na da hakan zai kaskantar da ni".

Wannan kalaman na Uniquepikin ya jawo hankalin masoya da dama, inda da dama daga cikin su ke tunanin ko martani mawakin ke mayar wa wasu mutane ko kuma da wani yake. Kawo yanzu dai mawakin bai baiyana da su waye yake ba, amma hoton da ya wallafa ya nuna mawakin a cikin farin ciki da kuma shiga irin ta mawaki a cikin nutsuwa.

A dan kwanakin baya ne Uniquepikin ya saki fefen bidiyo din wakar sa ta " Normal " tare da mawakiya kuma ma'akaciya a radio Queenzeeshaq, bidiyan wanda ba'a ga ita Queenzeshaq din a cikin ta ba, duk da dai ba su baiyana dalilin da ya sa ba a gan ta a ciki ba, ya samu aiki mai kyan gaske da labari mai daukan hankali. Kafin wakar "Normal" Uniquepikin ya fitar da bidiyan wakar sa mai suna "Inba tsoro ba" a karshen shekarar 2020 bayan daga dokar lockdown ta covid19.

Haka zalika mawakin na daga cikin mawakan da su ka kara a gasar Freedom Meku Award a shekarun baya tare da irin su AleeGee, Bmeri Aboki, Hanny Billy-O da sauran su. Za mu cigaba da bibiyan mawaki Uniquepikin dan jin ko martani mawakin ya ke mayar wa wasu ko kuma kawai dan jin dadi ya wallafa wannan hoto tare da kalaman da ya yi a ciki da harshen turanci.

Leave your comment