AleeGee na shirin sakin sabuwar waka.

Photo source: Ali zaki's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop kuma makadi "AleeGee" wanda aka wa lakabi da "Ali zaki" ya na shirin sakin sabuwar wakar sa a yan kwanakin nan a cikin shekarar 2021.

Sai dai mawakin ya na shirin sakin wakar tare da mawaki Adam A. Zango, Naziru sarkin waka ko Ali Jita a cikin sabuwar wakar. Mawakin ya baiyana hakan ne a tattaunawar sa da wakilin mu ta wayar talaho, bayan da ya daura fefen bidiyon da a ciki ya ke raira wakar a shafin sa na Instagram, AleeGee wanda ya na daya daga cikin mawakan da su ka fafata a cikin gasar Freedom Meku Award cikin shekaru hudu da su ka wuce inda ya zo na biyu a rukunin Hausa Hip Hop.

Wasu daga cikin manyan mawakan da su ka fafata a cikin gasar a wannan shekarar sun hada da Ali Jita, Hamisu Breaker, Bmeri Aboki da kuma Uniquepikin. Wasu daga cikin wakokin da AleeGee ya yi suna da su sun hada da "Alphabetical slaughter", "Sai ka yi" "Ko dan Mata" da kuma "Ali zaki".

Kuma AleeGee na daya daga cikin manyan mawaka da jihar Katsina inda nan ne asalin sa da kuma jihar Kano ke alfahari da shi. Muna dagon jiran mawaki AleeGee ya sanar da sunan wannan sabuwar wakar da kuma sunan mawakin da ya ke shirin su yi wakar tare.

Leave your comment