Mawakin "A bar raina mata "Zaaki Azzay" ya kara shekara daya a shekarun sa.

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Daya daga cikin mawakan da su ka fara Hausa Hip Hop a Nigeria kuma shaharren mawakin nan da ya yi wakar "A bar raina mata" wato "Zaaki Azzay" ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa"a satin nan da ya gabata a jihar Lagos. Mawakin ya wallafa hotunan sa ne a shafin sa na Instagram tare da yi wa kan sa fatan alheri a bisa kara shekara daya da ya yi a ranar 19 ga watan febureru na 2021.

Zaaki Azzay fitaccen mawaki, kuma mai gabatarwa a gidan talabijan ne shekara da shekaru tin bayan daukakar sa a duniyar waka. Wa su daga cikin wakokin da su ka yi fice a wakokin Zaaki Azzay sun hadar da "Mai ganga" da kuma "Na me go marry her".

Mawakin dan asalin kabilar " Tibi" da ke jihar Benuwe, mazaunin garin Lagos ne inda ya ke rayuwa tare da iyayen sa. Shima babban mawaki a Hausa Hip Hop B.O.C daga garin Bauchi ya daura hoton Zaaki Azzay tare da mai murna da kuma fatan alheri da zagayowar shekarar haihuwar sa.

Zaaki Azzay kamar yadda masoyan sa da ma duniya ta sheda, mawaki ne da ke da wani al'ada ko tsarin shidar kaya fari da baki wanda ita ce kalar tufafin da aka san kabilar sa da ita, sai kuma fitilar tocila da itama aka san mawakin da yawo da shi ko ina zai je kuma dare, safiya da rana haka ya ke kunna wannan fitilar.

Yawancin bukukkuwan manyan mutane ko yan siyasa a kasan nan ne mawakin ke gudanar da wasa kasancewa babba ne a masana'antar nishadi a Nigeria kuma daya daga wadan da su ka fara wakar gambara ta Hausa Hip Hop.

Leave your comment