Deezell na cigaba da shakatawa a Lagos

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Kano da kasar Amerika wato "Deezell", na cigaba da yawan shakatawa a jihar Lagos da ke kudancin Nigeria, tin bayan dawowan wakakin kasar nan a sabuwar shekarar nan ne Deezell ya ke yawon shakatawa tare da haduwa da wa su manyan mawaka a Lagos.

Inda a kwanakin baya aka hanko mawakin a cikin wani fefen bidiyo tare da producer " Baby fresh" manajan sa "Ceedeq" da kuma abokin sa kuma babban mawaki a Hausa Hip Hop hima wato " Dj Ab " a studio din "Marvin records" na "Don Jazzy".

Wannan ya faru ne kwanaki kadan bayan dawowar mawakin daga kasar Amurika tin bayan da aka saka dokar takaita yawan jiragen sama saboda da bulluwar cutar " corona virus " (covid 19).

Ko a satin nan an hango mawakin tare da shima shahararren mawakin Hausa Hip Hop "Kheengs" dan asalin jihar Niger a gaban taku a jihar Lagos din su na tsere kan baburan yashi, inda shi "Kheengs" din ya kife a kan babur din a lokacin da su ke tsaka da tseren.

Har yanzu dai mawakin bai baiyana dalilan sa na zuwa Lagos ba, in ban hotuna da bidiyon da ya ke wallafawa na shakatawa a shafukan sa na Instagram da Twitter.

Leave your comment