Classiq ya saki sabuwar kundin wakoki

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitacce mawaki daga masana'antar Hausa Hip Hop kuma mazaunin jihar Lagos da ke kudancin Nigeria ya saki sabuwar kundin wakokin sa a yau din nan Laraba 17 ga watan fabureru 2021. Kundin wakokin wanda ya kunshi wakoki kwaya bakwai ya samu aiki mai inganshi ne daga makada daban daban, sannan ya gaiyaci wasu mawakan a cikin kundin.

Da musalin karfe bakwai (7pm) na yanman yau ne mawakin ya sanar cewa kundin zai fito a dukkan shafukan sada zumunci da manhajojin da ke tallata wakoki da mawaka daban daban. "Class work" sunan kundin na Classiq kuma ita ce sabuwar aiki babba daga wannan shahararren mawakin Hausa Hip Hop da ake wa lakabi da "Captain Sama" ko "Arewa Mafia".

 

Classiq wanda ya yi wakoki da dama da mawakan kudancin Nigeria irin su Phyno, Reminisce, Vector da dai irin su mawaka yan asalin Arewa ma su waka a kudu irin su M.I Abaga, Jesse jagz da Ice Prince Zamani. Masoya dai tini su ka fara tofa albarkacin bakin su a yayin da su ke jiran su saurari mai kundin ya kunsa.

Leave your comment